logo

HAUSA

Jami’ar EDF: Matakan lardin Guangdong na Sin kan magance sauyin yanayi abin koyi ne

2023-12-04 10:43:54 CMG Hausa

Babbar jami'a a asusun kare muhalli na kasar Amurka (EDF) Angela Churie Kallhauge, ta bayyana cewa, lardin Guangdong na kasar Sin ne ke kan gaba wajen tsara manufofi game da batun sauyin yanayi da samun ci gaba ba tare a gurbata muhalli ba.

Jami’ar ta bayyana hakan ne a gyefen taron kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 28 (COP28) da ya gudana a Dubai na hadaddiyar daular Larabawa.

Ta lura cewa, lardin ya kasance mai tsayin daka, bude kofa, da kirkire-kirkire da kwarewa wajen magance matsalar sauyin yanayi da sauye-sauye zuwa ga samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, kuma asusun EDF ya shafe shekaru da dama yana hadin gwiwa da lardin kan magance matsalar sauyin yanayi, gami da gudanar da bincike, da samar da kwarewa, da shiga kasuwannin duniya, da gudanar da ayyukan kirkire-kirkire.

Ta ce, lardin ya gina hanyoyin kasuwanci masu inganci, gaskiya, da daidaito, a ganin ya cika alkawurran da ya dauka game da fitar da kololuwar iskar carbon da tsaka tsaki.

Ta bayyana cewa, kamfanoni a lardin sun himmatu wajen aiwatar da ayyuka marasa gurbata muhalli, da rage fitar da iskar carbon mai dumama yanayin duniya, ta hanyar kirkire-kirkire na fasaha da inganta matakan gudanarwa.

Angela Kallhauge ta ce, asusun EDF na fatan kara yin hadin gwiwa tare da lardin Guangdong a nan gaba, don tsara sabbin hanyoyin warware matsalar sauyin yanayi, da ba da gudummawa ga ci gaban tafiyar da harkokin duniya. (Ibrahim Yaya)