logo

HAUSA

Ministan kasa kuma ministan tsaron kasa, janar Salifou Modi ya karbi wata tagawar kasar Rasha a birnin Yamai

2023-12-04 11:13:58 CMG Hausa

Wani jirgin sojojin saman Rasha ya sauka a filin saukar jiragen kasa na kasa na Diori Hamani da ke birnin Yamai a ranar jiya da yamma 3 ga watan Disamban shekarar 2023.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoton.

Ita dai wannan ziyara, irinta ce ta farko da wasu manyan sojojin kasar Rasha suka kawo a kasar Nijar, tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata. Tagawar na karkashin jagorancin mataimakin ministan tsaron Rasha Evkurov tare da rakiyar wasu manyan sojojin Rasha. A rike cewa Mista Evkurov ya kai wata ziyarar aiki a ranar 2 ga watan Disamba a birnin Bamako na kasar Mali, kafin ya isa a ranar jiya 3 ga watan Disamba a Burkina Faso. A yayin wannan rangadi a wadannan kasashen biyu, babban jami’in sojan na Rasha ya tattauna tare da manyan sojojin kasashen biyu. Bayan wannan rangadi a kasashen biyu, da isowarsa a ranar ta jiya 3 ga watan Disamba da yamma a hedkwatar kasar Nijar, mista Evkurov ya samu tarbo daga ministan tsaron kasa Janar Salifou Modi.

A yayin wannan ziyara, bangaren kasar Rasha zai tattauna tare da bangaren Nijar kan bututuwan tsaro da na karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, musammun ma kan sha’anin yaki da ta’addanci da kasashen kungiyar kasashen Sahel AES suke fuskanta a kai a kai. Har ma da wasu batutuwan da suka jibanci makamashi da musanyar kwarewa.

Sai dai a rike cewa, wannan ziyara ta manyan sojojin Rasha ta zo washe garin bikin gabatar da takardar jakadanci a kasar Nijar da sabuwar jakadar kasar Amurka zuwa ga ministan harkokin wajen kasar Nijar Yaou Bakari Sangare.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.