logo

HAUSA

Al-Burhan: Ba za a amince da duk wata tattaunawar zaman lafiya da ba za ta cika burin Sudan ba

2023-12-04 10:19:19 CMG Hausa

Shugaban majalisar rikon kwaryar kasar Sudan, kuma babban kwamandan sojojin kasar Abdel Fattah Al-Burhan, ya bayyana a jiya Lahadi cewa, duk wata tattaunawar neman zaman lafiya da ba za ta iya cimma burin al'ummar kasar Sudan ba, to ba za a amince da ita ba.

Al-Burhan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron sojoji da aka gudanar a Wad Madani, babban birnin jihar Gezira. Yana mai cewa, “Ba za mu bari a kakkaba mana wata mafita daga kasashen waje ba."

Al-Burhan ya ce, "Mun je tattaunawar ce da zuciya daya, domin a cimma daidaito, cikakke da samar da zaman lafiya mai dorewa. Don haka, ya kamata duniya ta sani cewa, mafita tana cikin gida, wajibi ne su yi shawarwari da al'ummar Sudan."

Ya kuma sha alwashin cewa, sojojin Sudan za su ci gaba da yakin da suke yi na fatattakar dakarun kai daukin gaggawa (RSF).

Ya jaddada aniyar Sudan na yin hadin gwiwa da kasashen duniya, ya kuma yi maraba da zuwan sabon wakilin babban sakataren MDD a kasar Sudan Ramtane Lamamra. Yana mai gargadin cewa, ba sa son wakilin da yake goyon bayan wani bangare ko wata kungiya. (Ibrahim Yaya)