logo

HAUSA

Nijar da Burkina Faso sun sanar da janyewa daga kungiyar G5 Sahel

2023-12-03 17:16:51 CMG

Mahukuntan janhuriyar Nijar da na Burkina Faso, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa ta janyewar kasashen su daga kungiyar G5 Sahel, tun daga ranar 29 ga watan Nuwamban da ya shude.

Sanarwar da aka fitar a jiya Asabar, ta ce tun kafuwar kungiyar mai kunshe da kasashen Nijar, da Burkina Faso, da Mali, da Mauritania da Chadi, a ranar 19 ga watan Disamban shekarar 2014, har yanzu ta gaza cimma manufar kafa ta.

Tun da fari dai an kafa G5 Sahel ne da nufin tattara karfi waje guda, domin wanzar da tsaro da bunkasa yankin da kasashen suke. To sai dai a cewar sanarwar kasashen 2, bayan shekaru 9 da kafuwar kungiyar, ba ta haifar da wani abun a zo a gani ba.

Sanarwar ta kara da cewa "Ba zai yiwu G5 Sahel ta zama kungiyar dake kare muradun wasu kasashen waje ba, ko bin umarnin wasu bangarori na waje da sunan hadin gwiwa, musamman ganin yadda irin wadannan sassa na waje ke daukar mambobin ta tamkar wasu kananan yara, suna danne ‘yancin kasashen yankin na cin gashin kai”.

Kafin hakan a shekarar bara ma, kasar Mali ta janye daga kungiyar ta G5 Sahel.  (Saminu Alhassan)