Netanyahu ya ce wajibi ne a ci gaba da hare-hare ta kasa domin kubutar da Isra’ilawa da ake tsare da su
2023-12-03 17:32:12 CMG
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce ba zai yiwu a iya kubutar da Isra’ilawan da ake tsare da su a Gaza ba, muddin aka dakatar da kaddamar da hare hare ta kasa a sassan birnin. Netanyahu ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, bayan ya janye tawagar sa daga tattaunawar da ake yi a Qatar, game da batun tsagaita wuta da Hamas.
A cewar firaministan na Isra’ila, kafin karyewar yarjejeniyar kwanaki 7 ta tsagaita wuta a ranar Juma’a, an saki mutane 110, ciki har da ‘yan kasashen waje 24, sai dai har yanzu Hamas na ci gaba da tsare kusan mutane 135, da wasu mayaka a Gaza.
Ya ce ya umarci dakarun tsaron Isra’ila ko IDF, da su koma kaddamar da munanan hare hare. Sakamakon hakan, dakarun na Isra’ila sun kai hare hare kan wurare sama da 400, da wani harin sama mai muni kan Khan Yunis dake yankin kudanci, wanda a baya wuri ne da ake kallo a matsayin tudun-mun-tsira, da kuma Beit Lahia dake yankin arewa da zirin Gaza, da karin wasu wuraren.
Kaza lika, yayin wani taron manema labarai, ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant, ya danganta karyewar yarjejeniyar tsagaita wutar, da yadda Hamas ta ki amincewa ta saki wasu mata da kananan yara 15.
To sai dai a nasa martani, mataimakin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Saleh al-Arouri, ya musanta hakan, inda ya shaidawa kafar talabijin ta Al Jazeera a jiya Asabar cewa "Mun mika mata da kananan yara, kuma sauran fursunonin dake tsare a Gaza sojoji ne da fararen hula dake aikin soji.
Tuni dai aka hallaka mutane 15,200 a Gaza, tun barkewar rikicin dake wakana, kuma kaso 75 bisa dari cikin su yara ne, da mata da tsofaffi, kamar dai yadda hukumar kiwon lafiya ta Gaza ta bayyana.
Mahukuntan Isra’ila kuwa, cewa suka yi a nasu bangaren kusan mutane 1,200 hare haren ba zata na Hamas suka hallaka. (Saminu Alhassan)