logo

HAUSA

Shugaban Guinea-Bissau ya tabbatar da yunkurin kifar da gwamnatinsa

2023-12-03 17:34:04 CMG

Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, ya ce yunkurin juyin mulki ne ya haifar da arangamar da sojoji, da dakarun tsaron fadarsa suka yi a karshen mako.

Shugaba Embalo, wanda ya bayyana hakan da yammacin jiya Asabar, a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Osvaldo Vieira, bayan dawowarsa daga Dubai, inda ya halarci taron sauyin yanayi na COP28.

A cewar shugaban, mummunan fadan da ya barke tun daga daren Alhamis zuwa ranar juma’a a fadar mulkin kasar, ya biyo bayan yunkurin juyin mulkin sojoji ne da bai yi nasara ba, kuma dukkanin masu hannu a cikin sa za su yabawa-aya-zakin ta.   (Saminu Alhassan)