logo

HAUSA

Jagororin Afirka sun kaddamar da shirin bunkasa masana’antu marasa gurbata yanayi yayin taron COP28

2023-12-03 17:24:02 CMG

Shugaban kasar Kenya William Ruto, ya kira taron shugabannin kasashen Afirka mahalarta taron COP28 dake gudana yanzu haka, domin tattauna dabarun ingiza manufar bunkasa masana’antu marasa gurbata yanayi, da fannonin kasuwanci masu nasaba, da yayata dabarun dakile sauyin yanayi, da bunkasa ci gaban tattalin arziki maras gurbata yanayi a sassan Afirka.

An dai kaddamar da shiri na musamman game da wannan manufa, a gaban shugabannin da suka halarci taro, ciki har da shugabannin kasashen Angola, da Burundi, da Djibouti, da Ghana, da Kwadebuwa, da Mauritania, da Najeriya, da Senegal da Zambia da kuma jagoran taron COP28 Sultan Ahmed Al Jaber.

Cikin tsokacin da ya yi yayin kaddamar da shirin, shugaba Ruto ya ce "Shirin da aka kaddamar ya zamo ginshikin cimma burin yarjejeniyar Nairobi da aka amincewa, da farfado da tasirin sassa masu zaman kansu, na jagorantar ayyuka daban daban na bunkasa masana’antu marasa gurbata muhalli".

Kaza lika, mahalarta taron sun jaddada cewa, aiwatar da manufar bunkasa masana’antu marasa gurbata muhalli a Afirka, na da matukar muhimmanci wajen cimma burin hadin gwiwa na kare muhallin duniya baki daya.   (Saminu Alhassan)