logo

HAUSA

Mambobin COP 28 sun rattaba hannu kan sanarwa game da hatsi da aikin gona da yanayi

2023-12-02 16:39:10 CGTN HAUSA

 

Jiya Juma’a, a gun babban taro na COP 28 da aka yi a Dubai, mambobin kasashe 134 sun rattaba hannu kan sanarwar UAE na samar da hatsi cikin dogon lokaci da raya sha’anin gona mai dorewa da daukar matakin tinkarar sauyin yanayi, da zummar warware batun fitar da hayaki mai dumama yanayi, don kiyaye zaman rayuwar manoma a yankunan da suka fi fama da matsalar sauyin yanayi. An ce, tsarin samar da abinci shi ne muhimmin abu da aka tattauna a taron a wannan karo.

Sanarwar da aka rattaba hannu ta shafi yankuna ko kasashen da yawan mutanensu ya kai miliyan 5700, yayin da karfinsu na samar da hatsi ya kai kashi 70% na dukkan duniya da kuma kashi 76% na hayaki mai dumama yanayi na tsarin samar da hatsi a duniya. Mai karbar bakuncin taron a wannan karo wato hadaddiyar daular Larabawa ta sanar da cewa, al’ummar duniya na kebe kudade dalar miliyan 2500 don taimakawa samar da isasshen hatsi a duniya da tinkarar sauyin yanayi da ingiza kirkire-kirkire a bangare tsarin samar da abinci. (Amina Xu)