logo

HAUSA

Sin tana fatan Somaliya za ta kara karfin tsaron kasa

2023-12-02 16:10:00 CMG Hausa

A jiya 1 ga wata ne, kwamitin sulhun MDD ya zartas da daftarin kudurori uku, inda kudurin kawar da takunkumin hana jigilar makamai da aka kakabawa gwamnatin Somaliya ya samu kuri’un amincewa 14 da kuri’ar janye jiki daya daga kasar Faransa, kuma kuduri na biyu gaba daya aka yarda za a sake hana kungiyar ‘yan ta’adda ta al-Shabaab jigilar makamai.

Mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing ya yi tsokaci cewa, ana fatan Somaliya za ta yi amfani da damar domin kara karfin tsaron kasa, da kuma kyautata aikin tafiyar da makamai, ta yadda za ta dauki matakan yaki da ayyukan ta’addanci, tare kuma da tabbatar da kwanciyar hankali a kasar.

Kuduri na uku da aka zartas shi ne, za a kawo karshen aikin tawagar MDD a Sudan bisa bukatar gwamnatin kasar. Bangaren kasar Sin ya bayyana cewa, zai ci gaba da goyon bayan Sudan a kokarin da take yi don kiyaye ikon mulki da kwanciyar hankali da cikakken yankin kasa, kuma zai ci gaba da taka rawar gani domin tabbatar da ci gaban Sudan cikin lumana ta hanyoyi daban daban. (Jamila)