logo

HAUSA

Sin tana kokarin dakile sauyin yanayi

2023-12-02 15:44:09 CMG Hausa

A jiya Jumma’a 1 ga wannan wata ne aka kira taron kolin aikin dakile sauyin yanayi na babban taron sauyin yanayi na MDD da ake gudanarwa a birnin Dubai dake hadaddiyar daular Larabawa, inda manzon musamman kan harkokin dakile sauyin yanayi na kasar Sin Xie Zhenhua ya gabatar da ra’ayin kasar Sin a bangaren.

A cikin jawabinsa, Xie Zhenhua ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan aikin dakile sauyin yanayi, kuma tana aiwatar da tsare-tsaren da aka tsara, alal misali kololuwar fitar da sinadarin carbon zuwa shekarar 2030, da samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za a fitar da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060, haka kuma tana gyara tsarin masana’antu da makamashi da sufuri, tare kuma da kyautata tsarin kasuwanni domin tsimi da inganta makamashi.

Jami’in ya kara da cewa, adadin sinadarin carbon da kasar Sin ta fitar ya ragu a bayyane, kuma adadin motocin dake amfani da sabon makamashi da kasar Sin ta kera da kuma sayar da su ya kai matsayin kolin duniya a cikin shekaru takwas da suka gabata, wato kusan rabin motocin sabon makamashi suna tafiya a kasar Sin. Kana wutar lantarkin da ake samarwa bisa karfin iska da hasken rana shi ma ya kai sahun gaba a duniya a cikin ‘yan shekarun da suka wuce. Ban da haka, kasar Sin ta kasance kasa mafi saurin karuwar albarkatun gandun daji a fadin duniya.

Xie Zhenhua ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta kafa kasuwar sinadarin carbon mafi girma a duniya, lamarin da ya kara karfafa karfi da buri na rage fitar da sinadarin carbon na kamfanoni, a sa’i daya kuma, kasar Sin ta nuna kwazo da himma kan aikin tafiyar da harkokin dakile sauyin yanayi, kuma tana zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashe masu tasowa a fannin, tare kuma da samar da dabaru da matakai na ta ga tsarin tafiyar da harkokin dakile sauyin yanayi na kasa da kasa. (Jamila)