logo

HAUSA

Firaministan Cuba: Shawarar ziri daya da hanya daya za ta amfanawa duk duniya

2023-12-02 15:56:05 CGTN HAUSA

 

Kwanan baya, firaministan kasar Cuba Manuel Marrero Cruz ya shaidawa manema labaran CMG a Shanghai cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” da Sin ta gabatar a bude kofa take, wadda za ta amfanawa duk fadin duniya.

Ya ce, hadin kai da sauran kasashe kan wannan shawara ya bayyana basira da tunanin shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ya zarce moriyar Sin, ya mai da hankali kan muradun duniya ta bai daya, shawarar za ta ciyar da samun bunkasuwa da wadata a duniya cikin hadin kai.

Ya kuma kara da cewa, yana amincewa da hangen nesa a duniya da tsarin bude kofa da Sin take dauka, abin da ya baiwa kasashe masu tasowa damammaki masu kyau. Sin da Cuba na sada zumanta cikin dogon lokaci, suna fuskantar yanayi iri daya a fannoni daban-daban, kuma suna da dankon zumunci da mutunta juna. A ganinsa, dabaru masu kyau da Sin ta fitar abin koyi ne ga kasarsa, musamman ma matakan da suka dace da halin da kasarsa ke ciki, wajen raya tattalin arziki da al’ummar kasar.

Game da takunkumin da Amurka ke kakaba wa kasarsa, Manuel Marrero Cruz ya ce, abin ban dariya ne. Amurka ta kafa dokoki daban-daban don saka kasar cikin kangi, wadanda ke kawo babbar illa ga tattalin arziki da al’umma musamman ma fararen hula. Kwanan baya, Cuba ta mikawa MDD daftarin kudurin yin Allah wadai da Amurka, Sin tana amincewa da Cuba a wannan fanni har sau 31, yana matukar godiya ga goyon bayan da Sin ke ba ta, kuma ya bayyana gidoyar kasarsa ga shugaba Xi Jinping da dai sauran kasashen 186, a shirye suke suna goyon bayan a kawar da takunkumin da aka kakaba wa Cuba. (Amina Xu)