logo

HAUSA

An bude rumfar Sin kan babban taron sauyin yanayi na MDD a birnin Dubai

2023-12-01 09:57:04 CMG Hausa

A jiya ne, aka bude rumfar kasar Sin na babban taron bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 28 (COP28). An gudanar da bikin bude taron ne a yankin Blue Zone na birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ministan muhalli na kasar Sin Huang Runqiu, da manzon musamman na kasar Sin kan sauyin yanayi Xie Zhenhua, suka halarci bikin.

A yayin bikin bude taron, Huang Runqiu ya bayyana cewa, kasar Sin na nacewa ga samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da fitar da karancin sinadarin Carbon da samun ci gaba mai inganci, da aiwatar da dabarun raya kasa don tinkarar matsalar sauyin yanayi yadda ya kamata, da yin alkawarin kiyaye kololuwar iskar carbon, da shigar da shi cikin matakan kololuwar kiyaye yanayi, da wayewar muhalli da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa baki daya.

A shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da kasashen duniya, domin samun nasarar taron COP28, da sa kaimi ga kafa tsarin gudanar da harkokin yanayi na duniya cikin adalci, da ma'ana, da hadin kai da samun nasara, da gina duniya mai tsafta da kuma kyau tare.

Xie Zhenhua ya bayyana cewa, a matsayinta na babbar kasa mai tasowa dake sauke alhakin dake wuyanta, kasar Sin a ko da yaushe tana mai da hankali kan aiwatar da dabarun kiyaye sauyin yanayi. Kasar Sin ta zama babbar kasar da ke samar da na’urorin samar da wutar lantarki bisa karfin iska da baturan dake samar da wutar lantarki, lamarin da ya yi matukar rage farashin makamashin da ake iya sabuntawa a duniya tare da taimakawa kasashe masu tasowa samun makamashi mai tsafta, da za su dogaro a kai kuma mai araha. (Ibrahim)