logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi tir da matakan matsin lamba da nufin dakile tsarin jagoranci da ci gaban duniya

2023-12-01 10:32:06 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD, da sauran hukumomin kasa da kasa dake Vienna Li Song, ya yi Allah wadai da irin matakan matsin lamba da wasu sassa ke dauka, da nufin dakile managarcin tsarin jagoranci, da ci gaban duniya, wanda hakan ke haifar da koma bayan bunkasar zamantakewa da tattalin arzikin duniya.

Li wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin wani taron karawa juna sani mai taken "Matakan matsin lamba na kashin kai da mummunan tasirinsu ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin sassan kasa da kasa". Ya kara da cewa, Sin na tsaiwa tsayin daka wajen bunkasa sadarwa tsakaninta da daukacin sassa masu ruwa da tsaki, kana tana da burin shiga a dama da ita, wajen wanzar da halastaccen ikon raya kasashe masu saurin ci gaba da masu tasowa, kuma tana yayata dukkanin manufofi na hadin gwiwar kasashen duniya domin samar da ci gaba.

Taron wani bangare ne na ayyukan babban taron hukumar raya masana’antu ta MDD ko UNIDO, wanda ke gudana tun daga Litinin har zuwa Juma’ar nan.

Albarkacin babban taron na UNIDO, ofishin wakilcin Sin na MDD dake Vienna, ya ce a jiya Alhamis kasashe 10 da suka hada da Sin, da Rasha, da Iran da Cuba, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa game adawar su da matakan matsin lamba da wasu sassa ke aiwatarwa, wadanda suka ce na kawo tarnaki ga burin da ake da shi na cimma nasarar ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD nan zuwa shekarar 2030, tare da dakile matakan dunkule dukkanin sassa, da wanzar da ci gaban masana’antun duniya. (Saminu Alhassan)