Kusan mayaka 4,000 na BH da ’yan aware ne suka ajiye makamai a Kamaru tun daga 2018
2023-12-01 10:34:29 CMG Hausa
Kwamitin kula da batun kwance damara da sake shigar da tubabbun mayaka cikin al’umma na kasar Kamaru (NCDDR) ya ce tun daga shekarar 2018, jimilar mayaka 3,870 da suka hada da na BH da ’yan aware, sun ajiye makamansu a kasar.
Shugaban kwamitin NCDDR Francis Fai Yengo ne ya bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana ranar Laraba a birnin Yaounde, domin gabatar da wani sabon daftarin tsarin aiki na cibiyoyin kwamitin.
Ya kara da cewa, an sake shigar da galibin tubabbun mayakan cikin al’umma kuma al’ummomi da dama sun karbe su.
A cewarsa, aikin kwamitin NCDDR abu ne dake ci gaba da gudana, kuma akwai tarin ayyuka a gabansa. Yana mai cewa, sabon daftarin na kunshe da ka’idojin da za su taimaka musu gudanar da ayyukansu.
Ya kuma bayyana kokarin kwamitin na shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya a matsayin abu mai wahala, amma kuma ana samun nasarori. (Fa’iza Mustapha)