logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi bayani kan aikin kwamitin sulhu ga kasashe mambobin MDD

2023-12-01 19:28:15 CMG Hausa

Kasar Sin ce ta rike ragamar shugabancin karba-karba na kwamitin sulhu na MDD na watan Nuwamba. A ranar 30 ga watan Nuwamba, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya jagoranci wani taron takaita bayanai, inda ya gayyaci wakilan dindindin na kasashen Malta da Mozambique da su gabatar da ayyukan kwamitin sulhu na wannan wata ga kasashe mambobin MDD tare. Wakilai daga kasashe sama da 100 ne suka halarci taron. 

Zhang Jun ya bayyana cewa, rikicin Falasdinu da Isra’ila shi ne ajandar gaggawa ta kwamitin sulhu a wannan wata. Game da batun Falasdinu da Isra’ila, a ko da yaushe kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya, da adalci, da lamiri, kuma tana sa kaimi ga yayata matakai masu ma’ana da kwamitin sulhu ta dauka. Bangaren kasar Sin ya yi aiki tare da wakilan kwamitin sulhun MDD, wajen sa kaimi ga kuduri mai lambar 2712. Wannan shi ne kuduri na farko da kwamitin sulhun ya zartar kan batun Isra'ila da Falasdinu tun karshen shekarar 2016, kuma kudurin farko da kwamitin sulhun ya zartar tun bayan barkewar sabon rikici tsakanin Falasdinu da Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba. (Yahaya)