logo

HAUSA

Fasahohin zamani na taimakawa raya kauyuka da aikin gona a kasar Sin

2023-12-01 20:39:37 CMG Hausa

A cikin shirin yau za mu mai da hankali kan yadda kasar Sin ke amfani da fasahohin zamani wajen raya yankunan karkara na kasar, gami da aikin gona.

Filayen gona a kasar Sin ba su da yawa, idan an kwatanta da dimbin al’umma da ake da su a kasar. Saboda haka, an fi samun manoman da suke kula da kananan gonaki nasu a kasar, lamarin da ya hana a yi amfani da manyan na’urorin aikin gona na zamani. Har zuwa yanzu, ingancin aikin gona ta fuskar samar da kayayyaki na kasar Sin bai wuce kashi 25.3% na ingancin sauran fannonin kasar, wadanda ba su shafi aikin gona ba. Ganin haka ya sa gwamnatin kasar Sin daukar kwararran matakai a wadannan shekaru, don tabbatar da zamanantar da aikin gona, da ci gaban harkoki a kauyukan kasar. (Bello Wang)