logo

HAUSA

Isra'ila ta ci gaba da yakar Hamas

2023-12-01 16:08:04 CMG Hausa

Rahotanni daga rundunar tsaron Isra’ila na cewa, Isra’ila ta ci gaba da yakar kungiyar Hamas a zirin Gaza.

Wata majiyar lafiya a zirin Gaza ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua Jumma’ar nan cewa, harin da Isra'ila ta kai a zirin Gaza, ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 10 tare da jikkata wasu da dama.

A yau da misalin karfe 7 na safe agogon wurin ne, yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin Isra'ila da Hama ta kawo karshe. (Ibrahim Yaya)