logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da takwarorinsa na kasashen Larabawa da na musulmi

2023-11-30 20:37:59 CMG HAUSA

 

Jiya Laraba, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da manyan jami’ai masu kula da harkokin waje na kasashen Qatar da Jordan da Saudiyya da Palesdinu da Turkiya da Masar da Indonesiya da Malaysia da kasar hadaddiyar daular Larabawa da babban sakataren AL Ahmed Aboul Gheit a hedkwatar MDD dake New York.

Wang Yi ya ce, game da batun rikicin Palasdinu da Isra’ila, Sin da kasashen Larabawa da kasashen musulmi suna da matsaya daya, suna yabawa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Qatar da Masar suka sa kaimi cimmawa. Sin na fatan kara hadin gwiwa da bangarori daban-daban, da ingiza kwamitin sulhu da ya dauki mataki mai amfani don sauraron ra’ayin kasashen Larabawa da na musulmi, ta yadda za a dauki karin mataki mai aminci.

Ban da wannan kuma, bayan an kammala babban taro dangane da batun Palasdinu da Isra’ila da kwamitin sulhu ya gabatar, Wang Yi ya shaidawa manema labarai cewa, manufar kafa kasashe biyu ita ce hanya daya tilo da za a bi wajen warware wannan matsala. Sin ta yi kira da a gudanar da taro mafi karfi da inganci don wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa, ta yadda za a ingiza warware batun Palasdinu cikin adalci da daidaici a duk fannoni kuma na dogon lokaci. (Amina Xu)