An gudanar da taron yankin Afirka na WTCF a Tunisiya
2023-11-30 12:36:42 CMG Hausa
An gudanar da taron yankin Afirka na tarayyar biranen yawon shakatawa na kasa da kasa wato WTCF a Hammamet, birnin dake gabar teku a gabashin kasar Tunisiya jiya Laraba.
Jigon taron shi ne “sabon zamanin hadin gwiwar yawon shakatawa tsakanin Sin da Afirka”, wanda ke da nufin sa kaimi ga ci gaban hadin gwiwar yawon shakatawa tsakanin Sin da kasashen Afirka da inganta mu’ammala da hadin gwiwa tsakanin kamfanonin yawon shakatawa na Sin da kasashen Afirka.
Ministan yawon shakatawa na Tunisiya, Mohamed Moez Belhassine ya bayyana a gun bikin bude taron cewa, a bana za a habaka tsarin ba da visa kyauta ta kasar Tunisiya, ba ma kawai ga tawagar masu yawon bude ido na kasar Sin ba, har ma ga daidaikun masu yawon bude ido, tare da fatan samun karin Sinawa masu yawon bude ido zuwa kasar Tunisiya. A matsayinta na kasar dake cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya", kasar Tunisiya tana son hada kai da kasar Sin don kara raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannin yawon shakatawa.
A jawabinsa, mataimakin babban sakataren tarayyar biranen yawon shakatawa na kasa da kasa, Li Baochun ya bayyana cewa, kasar Sin mai bude kofa da samun ci gaba na fatan raya hadin gwiwar yawon shakatawa tare da karin kasashen Afirka, tare da sa kaimi ga hadin gwiwar yawon shakatawa tsakanin Sin da kasashen Afirka zuwa wani babban matsayi.
Shugaban hukumar yawon shakatawa ta kasar Tunisiya ya bayyana yayin wata hira da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Sin babbar kasuwa ce mafi muhimmanci a fannin yawon bude ido a duniya, kuma yana da kwarin gwiwa game da hadin gwiwa da samun bunkasuwa a nan gaba tsakanin Tunisiya da Sin a fannin yawon bude ido.(Safiyah Ma)