logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta hallaka kusan mutum 270 a yankin hakon Afirka

2023-11-30 10:24:32 CMG Hausa

Wani rahoto da cibiyar ICPAC mai hasashe da lura da sauyin yanayi karkashin kungiyar raya gabashin Afirka ta fitar, ya nuna cewa kusan mutane 270 ne suka rasa rayukan su, kana sama da 900,000 suka rasa matsugunan su, sakamakon ambaliya, da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa a yankunan kahon Afirka.

Rahoton wanda ICPAC ta fitar a jiya Laraba, ya ce kasashen Kenya, da Habasha da Somalia ne kan gaba, wajen fuskantar ibtila’in mai nasaba da mummunan tasirin sauyin yanayi na “El Nino”, da banbancin yanayin zafin sassan tekun Indiya. Kaza lika rahoton ya jaddada cewa, cikin sama da wata guda, kasashen Somalia da Kenya na fuskantar saukar ruwan sama fiye da kima, wanda ke da nasaba da sauyin yanayi.

Wannan ibtila’i dai ya hallaka kusan mutane 100 a Somalia, da 120 a Kenya, da kuma mutane 46 a Habasha. Yayin da kuma lamarin ya raba mutane 700,000 da muhallan su a Somalia, da mutum 136,000 a Kenya, da kuma kusan mutane 50,000 a Habasha.

Rahoton cibiyar ICPACn ya ce adadin mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa ya kai sama da mutum miliyan 1.5 a Somalia, da mutum 950,000 a Kenya da kuma mutum 101,890 a Habasha. Baya ga asarar rayuka, ibtila’in ya kuma lalata gonaki da dama a kasashen 3.  (Saminu Alhassan)