logo

HAUSA

AU ta yi kira ga kasashen Afirka da su kawo karshen cin zarafin mata da 'yan mata

2023-11-30 10:47:58 CMG Hausa

 

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat ya yi kira ga kasashen Afirka, da su dauki kwararan matakai, domin kawo karshen cin zarafin mata da 'yan mata.

Faki ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a yammacin ranar Talata a yayin bikin kwanaki 16 na fafutukar kawo karshen cin zarafin mata da ’yan mata, wanda ake gudanarwa duk shekara daga ranar 25 ga watan Nuwamba zuwa 10 ga watan Disamba.

Ya ce, idan har ana fatan tabbatar da makomar da tashin hankali ba zai zama wani shinge ga karfafa tsaro na mata da ’yan mata ba, ya kamata a gaggauta canza kudurin hadin gwiwa da aka cimma zuwa matakai na zahiri, wanda zai kai ga kare al'ummomin nahiyar zuwa wurare masu aminci, daidaito da za su kunshi kowa da kuma kare hakkin mata da ’yan mata.

Faki ya bayyana cewa, bikin na bana ya zo daidai da cika shekaru 20 da kafuwar yarjejeniyar Afirka game da kare hakkin bil adama da al'ummar Afirka kan hakkin mata a Afirka, yana mai jaddada bukatar yin hadin gwiwa, wajen kawar da cin zarafin mata da ’yan mata a fadin nahiyar Afirka. (Ibrahim Yaya)