logo

HAUSA

Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka ya rasu yana da shekaru 100

2023-11-30 11:11:11 CMG Hausa

 

Rahotanni na cewa, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger ya rasu a gidansa dake jihar Connecticut, yana da shekaru 100 a duniya.

An haife shi a kasar Jamus a shekara ta 1923, Kissinger ya rasu ya bar matarsa Nancy Kissinger mai shekaru kusan 50, da 'ya'ya biyu da ya haifa a aurensa na farko, wato David da Elizabeth, da kuma jikoki guda biyar.

Kissinger ya ziyarci kasar Sin fiye da sau 100. (Ibrahim Yaya)