logo

HAUSA

Najeriya na fatan samun bunkasuwar kashi 3.76 na tattalin arziki a shekarar 2024

2023-11-30 10:47:02 CMG Hausa

 

A jiya Laraba ne, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da kudurin kasafin kudi na shekarar 2024 ga zaman hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar da aka gudanar a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, wanda ke da nufin ganin an samu bunkasar kashi 3.76 cikin 100 a GDPn kasar, lamarin dake zama wani muhimmin mataki na farfado da tattalin arzikin kasar.

Kudurin kasafin kudin mai taken “sake farfado da fata”, ya kunshi Naira tiriliyan 27.5 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 34.8.

Shugaba Tinubu ya bayana cewa, gwamnatinsa na sa ran tattalin arzikin kasar zai bunkasa da abin da bai gaza kashi 3.76 cikin 100 ba. Ana kuma sa ran hauhawar farashin kayayyaki, za ta daidaita zuwa kashi 21.4 cikin 100 a shekarar 2024. Ya kara da cewa, babban burin gwamnati a shirye-shiryen kasafin kudin shekarar 2024, shi ne ci gaba da dorewar harsashin ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

Ya kuma jaddada fatan samar da tsaron kasa da na cikin gida, da samar da guraben ayyukan yi, da daidaita tattalin arzikin kasa, da inganta yanayi na zuba jari, da bunkasa hanyoyin samun kudin shiga ga ’yan kasa, da rage talauci, da tabbatar da zaman lafiya a matsayin wasu manyan abubuwan da gwamnatin ta sanya gaba a kasafin kudin shekarar 2024.

Tinubu ya kuma yi karin haske cewa, kan yadda aka amince da tsarin farashin mai na dalar Amurka 77.96 kan kowace ganga. Wannan shawara, tare da kiyasin hako mai a kullum na ganga miliyan 1.78, na nuni da yadda aka yi nazari sosai, kan yadda kasuwannin mai na duniya ke tafiya. Yana mai jaddada muhimmancin yadda kasafin kudin zai taimaka wajen daidaita yanayin da ake ciki a kasuwannin mai na kasa da kasa.

Ana sa ran majalisar dokokin kasar za ta tantance tare da amincewa da kasafin kudin na Naira tiriliyan 27.5, kafin daga bisani ta mayar wa shugaban kasar. (Ibrahim Yaya)