logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi wa Biden ta’azziyar rasuwar Henry Kissinger

2023-11-30 19:46:26 CMG HAUSA

 

Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikawa takwaransa na kasar Amurka Joe Biden sako don nuna juyayi ga rasuwar Henry Kissinger, a cikin sakon, a madadin kansa da gwamnati da jama’ar kasar Sin, Xi Jinping ya bayyana matukar bakin ciki da juyayi ga rasuwar Doctor Henry Kissinger, tare da gai da iyalansa.

Xi Jinping ya bayyana cewa, Henry Kissinger, shahararren ‘dan siyasa ne a duniya, kuma tsohon abokin al’ummar Sinawa ne mai dangantakar kut da kut. Sin na fatan hadin kai da Amurka wajen ingiza sha’anin sada zumunta tsakanin al’umommin kasashen biyu da kuma ciyar da dangantakar kasashen biyu gaba, ta yadda za a amfanawa mutanen bangarorin biyu da taka rawa wajen shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwar duniya yadda da ya kamata. (Amina Xu)