logo

HAUSA

Messi ya lashe Ballon d'Or na 8 yayin da Bonmati ta lashe kyautar a ajin mata

2023-11-29 20:23:39 CRI

Tauraron kwallon kafa dan kasar Argentina Lionel Messi, ya lashe kyautar Ballon d'Or da ake baiwa dan wasa mafi hazaka a duk shekara, inda a wannan karo Messi ya karbi kyautar a karo na 8, a bikin da ya gudana a birnin Faris na Faransa. A ajin mata kuwa, ‘yar wasan kasar Sifaniya Aitana Bonmati ce ta karbi kambin na Ballon d'Or.

Ana ganin Messi ya lashe Ballon d'Or na bana ne sakamakon irin gudummawar da ya baiwa Argentina, wajen lashe gasar cin kofin duniya da kasar Qatar ta karbi bakunci a bara, inda ya zura kwallaye 7 a raga, kuma aka bayyana shi a matsayin dan wasa mafi hazaka a gasar ta Qatar.

Messi ta lashe Ballon d'Or a shekarun 2009, da 2010, da 2011, da 2012, da 2015, da 2019, da 2021 da kuma na bana wato 2023.

Da yake bayyana farin cikin sa game da lashe lambar yabon ta bana, Messi ya ce “Wannan kyauta ce ga daukacin tawagar mu bisa nasarar da muka yi. Mun jima muna fatan lashe kofin duniya. Ina godewa dukkanin wadanda suka taimaka har muka lashe wannan kofi na duniya. Ina kuma sadaukar da wannan kofi ga tauraron kwallon kafar kasar mu Diego Maradona, wanda ya rasu a shekarar 2020, wanda da yana raye a bana zai cika shekaru 63 da haihuwa. Barka da zagayowar ranar haihuwa Diego. Wannan naka ne!” Messi ya fadi hakan yayin da yake daga kyautar ta Ballon d'Or.

Baya ga Messi, an baiwa dan kwallon Norway Erling Haaland kyautar karramawa ta 2, bisa nasarar da ya samu ta lashe kofin zakarun turai na UEFA, da kofin Firimiyar Ingila, da FA Cup tare da kungiyar Manchester City. A matsayi na uku kuwa, dan wasan Faransa Kylian Mbappe ne ya karbi kyauta, bayan da a yayin gasar cin kofin duniya na Qatar ya lashe takalmin zinari.

A ajin mata ‘yan kwallo kuwa, Aitana Bonmati daga Sifaniya ce ta lashe kyautar Ballon d'Or ta bana, sai kuma ‘yar wasan kasar Australia Sam Kerr da ta zo na biyu, yayin da Salma Paralluelo daga Sifaniya ta zo na 3, bayan da kungiyar Sifaniyan ta lashe kofin duniya na mata a watan Agustan da ya gabata.

A daya bangaren kuma, dan wasan Ingila Jude Bellingham, ya lashe lambar yabo ta dan wasa mafi hazaka dan kasa da shekaru 21, yayin da aka baiwa Haaland lambar karramawa, ta dan wasan gaba mafi kwarewa na shekarar bana. Sai kuma Emiliano Martinez daga Argentina, wanda ya lashe kyautar Lev Yashin, ta mai tsaron gida mafi kwarewa.

Tsofaffin zakarun wasannin motsa jiki na Sin na tallafawa sabbin ‘yan wasa masu tasowa

Da yawa daga Sinawa da suka yi fice a wasannin motsa jiki a gasanni daban daban, a yanzu haka suna taimakawa ‘yan wasa masu tasowa, don haka duk da cewa sun kammala shiga gasanni amma bajimtar su, da gudummawar da suke bayarwa na ci gaba da amfanar al’umma.

Irin wadannan Sinawa da suka lashe lambobin yabo a gasannin kasa da kasa, bayan sun yi ritaya, su kan koma aikin horas da ‘yan wasa. A halin yanzu, suna reno da baiwa sabbin ‘yan wasa horon sanin makama, inda suke kasancewa abun misali yayin gasannin da matasan ‘yan wasan ke shiga, kamar gasar farko ta matasa da aka bude a lardin Guangxi Zhuang mai cin gashin kan sa.

Daya daga irin wadannan masu horas da ‘yan wasa mai suna Huang Shanshan, ta yi tsokaci bayan rashin nasarar tawagar da take jagoranta a Xiamen, a wasan tsalle kan raga ko trampoline, inda ta ce a halin yanzu, takara na kara tsananta tsakanin ‘yan wasan motsa jiki dake sassan kasar Sin.

Huang, mai shekaru 37 a duniya, wadda ta taba lashe lambar tagulla a ajin mata na gasar trampoline a Olympics na birnin Athens, a shekarar 2004, ta ce “A da can, nan lardin Fujian ne cibiyar wasanni, amma a yanzu larduna irin su Shanxi, da Jiangsu, da Zhejiang suna kara yin fice a fannonin wasannin motsa jiki. Sai dai duk da haka, muddin mun ci gaba da aiki tukuru, nan zuwa shekaru 4 ko 8 za su cimma sabbin nasarori".

Bayan ritaya daga gasanni a shekarar 2013, Huang, ta koma horas da ‘yan wasa, inda ta jagoranci babbar tawagar ‘yan wasa masata ta kasa, kana daga baya ta jagoranci tawagogin lardinta na Fujian, ciki har da tawagar Fuzhou da Xiamen. Karkashin shugabancin ta, tawagogin wadannan wurare sun shiga an dama da su a gasanni daban daban, kamar gasar lashe kofin matasa na kasar Sin na shekarar 2015.

Huang ta kara da cewa "Ajin gasannin matasa ya sha banban da irin gasannin da na halarta. Gasar matasa na da kayatarwa sosai. Ina fatan masu shiga wannan wasa na tsallen trampoline za su more dadin wasan”.

Shi ma yayin da yake kallon dan wasan da ya horas wato Wu Jian, koci Dong Bin, wanda ya taba lashe lambar tagulla a wasan tsallen trampoline, a gasar Olympics ta 2016, ya cika da farin ciki da alfahari. A cewar Dong "Yayin da nake kallon ‘yan wasa dake fafatawa a filin wasa, na kan ji kamar ma na fi su damuwar cimma nasara".

An haifi matashi Wu ne a shekarar 2004, ya kuma tashi da hazaka wadda ke nuna yiwuwar zai cimma nasarori. Koci Dong ya lura da irin karsashi da matasa da yawa da yake horaswa ke da shi a fannin wasannin motsa jiki.

A cewar sa "Wasanni abubuwa ne dake nishadantar da ni. Suna sanyawa na rika gano kuskuren ‘yan wasa na, da ma nawa kuskuren. Bayan gasa, ya zama wajibi mu ci gaba da kokari tare da kyautata kwarewar mu"

Wasu karin sanannun ‘yan wasa na kasar Sin, irin su Wang Ke, wanda a baya ya lashe lambar yabo ta duniya har karo 4, a wasannin tsalle tsalle da sarrafa gabobin jiki, kuma malamin makaranta a jami’ar koyar da wasanni dake birnin Tianjin, shi ma ya halarci gasar ta lardin Guangxi Zhuang. Wang ya jagoranci tawagar dalibai 30 daga Tianjin, domin shiga wasannin motsa gabobi da aka shirya.

Da yake karin haske ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Wang ya ce "Wadannan wasanni ne dake da asali mai karfi daga makarantu, wanda hakan ya ba ni damar kara inganta kwarewa ta a fannin horas da matasan ‘yan wasa".

A bangaren sa kuwa, jagoran ‘yan wasan zamiya ta “roller skating” daga Taiyuan, kuma tsohon shugaban tawagar kasar Sin a wasan Chen Bin, nanata mahangar Wang ya yi don gane da ci gaban wasannin motsa jiki na matasa.

Shi kuwa Liu Huixia, wanda ya jagoranci tawagar matasa ‘yan wasan linkaya ta birnin Wuhan cewa ya yi "Tsofannin ‘yan wasan motsa jiki na Sin na samar da horo mai inganci ga matasan ‘yan wasa, kana suna zamewa matasan abun koyi. Masu horas da ‘yan wasa na da muhimmancin gaske ga tawagogin ‘yan wasa. Idan koci ya tantance kwazon ‘yan wasan sa, zai iya kashe karin lokaci da kwazon horas da su. A daya bangaren kuma, idan ‘yan wasa suka lura da ci gaban da suke samu, hakan zai kara musu kwarin gwiwa ". Liu ya fadi hakan ne game da tasirin horaswa mai inganci, da kuma irin ci gaban da take haifarwa.