Real Madrid ta ci gaba da kasancewa a saman teburin La Liga bayan da Girona da Athletic Bilbao suka yi kunnen doki
2023-11-29 20:13:16 CRI
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid mai taka leda a Sifaniya, ta ci gaba da kasancewa a saman teburin zakarun kasar wato La Liga, bayan da takwarorin ta Girona da Athletic Bilbao sun tashin kunnen doki da ci 1 da 1 a daren ranar Litinin, kuma da hakan Real Madrid ta sha gaban Girona a gasar ta La Liga, yayin da Athletic Bilbao ta fada matsayi na 5.
A wasan na ranar Litinin, dan wasan Girona Viktor Tsygankov ne ya zura kwallo a ragar Athletic Bilbao a cikin minti na 55 da take wasa, kafin kuma Inaki Williams na Bilbao ya farke kwallon bayan mintuna 12.
Duk da cewa an ci kwallayen ne bayan hutun rabin lokaci, amma ‘yan wasan kungiyoyin biyu sun rika kaiwa juna hare hare tun ma kafin tafiya hutun rabin lokacin.
Gorka Guruzeta, ya samu damar jefa kwallo ta farko ga Athletic tun cikin minti na 5 da take wasa, amma ya gaza yin hakan, inda ya buga kwallon da mai tsaron gidan Girona Paulo Gazzaniga ya cafe.
Kaza lika, dan wasan gefe na Girona Savio, ya yi ta kai hare-hare, da taimakawa kungiyarsa ta kai ga cin kwallaye, amma shi ma hakansa ba ta kai ga ruwa ba, har aka juya hutun rabin lokaci.
Bayan hutun rabin lokaci, ‘yan wasan Athletic sun kara himma, tare da kai hare hare daban daban, sai dai duk da hakan Girona ce ta fara yin nasarar jefa kwallo a ragar Athletic, mintuna 10 bayan komawa daga hutun rabin lokaci.
Duk da Girona ta samu maki daidai da na Real Madrid, ta ci gaba da zama a matsayi na 2 a kan teburin gasar da banbancin yawan kwallaye, yayin da ita kuma Athletic ta yi kasa zuwa matsayi na 5, amma duk da haka, ta samu maki guda, sakamakon kunnen doki da suka tashi tare da abokiyar fafatawarta Girona, kuma tuni Girona din ta samu maki 11 cikin wasanni 13 da ta buga a kakar bana.
Hukumar FIBA ta shirya gasar samar da guraben shiga Olympic
Hukumar shirya gasar kwallon kwando ta kasa da kasa FIBA, ta sanar da shirin ta na gudanar da gasar fitar da kungiyoyin da za su fafata, a gasar Olympic ajin maza ta 2024.
Za a buga wasannin fitar da zakarun da za su fafata a gasar ta Olympic ne a birnin Piraeus na kasar Girka, da Piraeus na Latvia, da Riga na Puerto Rico, da San Juan da Valencia na Sifaniya, a tsakanin ranaikun 2 zuwa 7 ga watan Yulin shekarar 2024 dake tafe.
Jimillar kungiyoyin kasashe 24 ne za su fafata a gasannin, ciki har da 19 da suka samu gurbi yayin gasar cin kofin duniya na shekarar 2023 da ya gudana a Philippines, da Japan da Indonesia, da kuma wasu karin kasashen 5, wadanda suka buga wasannin neman gurbi a watan Agusta.
Bisa tsarin FIBA, kungiyoyin da suka yi nasara a gasannin da za a buga ne za su halarci gasar Olympic da birnin Paris zai karbi bakunci a shekarar 2024, bayan da mai masaukin baki Faransa, da wasu kungiyoyin 7 suka riga suka samu gurbi.
Yanzu haka dai hukumar FIBA na shirin gudanar da wala-walar fitar da rukunonin da za su fafata a gasar dake tafe.