logo

HAUSA

Isra’ila ta saki Falasdinawa 30 a rana ta 5 ta tsagaita wuta

2023-11-29 10:42:22 CMG Hausa

 

Rahotanni na cewa mahukuntan Isra’ila sun saki Falasdinawa 30 dake tsare a wasu gidajen kurkukun kasar, ciki har da mata 15 da yara kanana 15, karkashin yarjejeniyar musayar fursunoni da Isra’ilan ta kulla da kungiyar Hamas ta Falasdinawa.

A cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua wanda ya shaida aukuwar hakan, da yammacin jiya Talata aka saki Falasdinawan 30, daga gidan yarin Ofer na Isra’ila, wanda ke birnin Ramallah kusa da gabar yamma da kogin Jordan.

Wannan ne dai karo na 5 da Isra’ilan ta saki gungun Falasdinawa daga gidan yarinta. Kafin hakan, ita ma tawagar dakarun Hamas ta Al-Qassam, ta mika rukuni na 5 na Isra’ilawa da take tsare da su ga tawagar agajin jin kai ta kasa da kasa ko Red Cross. Gwamnatin Isra’ila ta tabbatar da karbar mutane 12 da ake tsare da su a zirin Gaza, ciki har da ’yan kasarta 10, da wasu ’yan Thailand 2.

A wani ci gaban kuma, ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar, ta ce an amince da kara kwanaki 2, a wa’adin tsagaita bude wutar da a baya aka tsara karewarsa jiya Talata.

A jiya Talata, yayin zantawa ta wayar tarho, tsakanin shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi da takwaransa na Tunisia Kais Saied, shugabannin 2 sun jaddada bukatar tsagaita wuta a zirin Gaza. Suna masu fatan za a gaggauta aiwatar da matakan samar da agajin jin kai ga al’ummar Gaza ta dukkanin hanyoyin da suka kamata, tare da azamar warware dukkanin batutuwan da suka shafi Falasdinawa bisa adalci.   (Saminu Alhassan)