Masana kimiyya da matasan Afirka su yi kira da a gaggauta komawa amfani da makamashi da ake iya sabuntawa
2023-11-29 10:30:06 CMG Hausa
Masana kimiyya 50, da matasa sama da 2,000 daga kasashen Afirka 30, sun yi kira da a gaggauta komawa ga amfani da nau’o’in makamashi da ake iya sabuntawa, maimakon masu fitar da iska mai dumama yanayi, da nufin inganta matakan nahiyar na shawo kan kalubalen sauyin yanayi.
Sassan sun yi kiran ne cikin wata budaddiyar wasika da suka fitar a birnin Nairobin kasar Kenya da yammacin ranar Litinin, wadda ta bayyana cewa, juriyar nahiyar Afirka ga matsalolin sauyin yanayi za ta tabbata ne kadai, idan har kasashenta sun cimma nasarar kawar da amfani da makamashin da ake konawa, wanda kan fitar da iska mai dumama yanayi.
An dai fitar da wasikar ne ga shugabannin kasashen Afirka, gabanin taron sauyin yanayi na MDD da zai gudana, daga gobe Alhamis zuwa 12 ga watan Disamba mai kamawa, a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa.
Cikin wannan wasika, masana kimiyyar sun koka game da yadda ake ta hankoron hako albarkatun mai da iskar gas, da kwal a sassan nahiyar, matakin da a cewarsu na iya haifar da tsaiko ga manufar komawa amfani da makamashi maras dumama yanayi.
Da yake tsokaci kan batun, farfesa Corneille Ewango Ekokinya, na jami’ar Kisangani dake janhuriyar dimokaradiyyar Congo, ya ce yana da muhimmanci a dakatar da zuba sabon jari a fannin sarrafa makamashin da ake konawa, ta yadda nahiyar Afirka za ta sauke nauyinta na shawo kan sauyin yanayi.
Farfesa Ekokinya ya kara da cewa, sauya akalar makamashin da ake amfani da shi a kasashen Afirka zuwa marasa dumama yanayi, da samar da matakan inganta juriya, da hade dukkanin sassa, za su taimaka matuka wajen dakile fitar da nau’o’in iska mai dumama yanayi, wadanda su ne ke kara ta’azzara mummunan tasirin sauyin yanayi, kamar fari, da ambaliyar ruwa da karuwar matukar zafi. (Saminu Alhassan)