logo

HAUSA

Gwamnatin Saliyo ta bayyana matsalar da ta faru ranar Lahadi a matsayin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba

2023-11-29 11:09:18 CMG

Gwamnatin Saliyo ta bayyana cewa, hare-haren da wasu mutane dauke da makamai suka kaddamar kan barikin soji da wasu wurare ranar Lahadin da ta gabata a Freetown, babban birnin kasar, a matsayin wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba.

Ministan yada labarai da ilimantar da jama'a Chernor Bah ne ya bayyana hakan, a yayin wani taron manema labarai, inda ya ce an kama mutane 14 da suka hada da sojoji 13 da farar hula guda.  Ya kara da cewa, yanzu haka wadanda ake zargin suna taimakawa ‘yan sanda a binciken da suke yi.

Idan ba a manta ba, da sanyin safiyar ranar Lahadin da ta gabata ce, wasu mutane dauke da makamai suka kai hari kan barikin sojoji da ke Wilberforce da wasu wurare da suka hada da cibiyar gyaran hali dake kan titin Pademba, lamarin da ya kai ga fasa gidan yarin.

A halin yanzu ‘yan sanda na ci gaba da farautar fursunonin da suka tsere, inda wasunsu bisa radin kansu suka mika kansu ga hukumomin gidan yarin. (Ibrahim)