Jakadan Sin a Nijar ya gana da shugaban kwamitin tsaron kasar
2023-11-29 19:08:04 CMG Hausa
A ranar 28 ga watan Nuwamba, jakadan kasar Sin a Nijar Jiang Feng ya gana da Abdourahmane Tchani, shugaban kwamitin tsaron kasar Nijar, inda suka yi musayar ra’ayi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Jiang Feng ya gode wa shugaba Tchani da ya tarbe shi, ya kuma bayyana cewa, ko da yake kasashen Sin da Nijar suna da nisan mil dubu tsakanin juna, amma al’ummomin kasashen biyu na da kyakkyawar alaka na asali. Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijar na ci gaba da bunkasa, kuma kaddamar da aikin mai na Nijar Agadem mataki na biyu, wata babbar nasara ce ta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, wanda zai sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar Nijar.
Abdourahame Tchiani ya bayyana cewa, Nijar da Sin abokai ne na kwarai, kuma hadin gwiwar da suke yi a fannoni daban-daban, musamman a fannin albarkatun man fetur, ya samar da sakamako mai kyau, wanda ya haifar da fa'ida ta gaske ga al'ummar Nijar. Nijar a shirye take ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin, da sa kaimi ga ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Yahaya)