logo

HAUSA

Matakan Sin na taimakawa kamfanoni masu zaman kansu

2023-11-29 07:40:32 CMG Hausa

Mahukunta a kasar Sin sun kaddamar da wani shiri na karfafa ayyukan samar da hidimomin kudi ga kamfanoni masu zaman kansu, a wani mataki na taimakawa ci gaban wadannan sassa.

Wata sanarwar da hukumomi 8 da suka hada da babban bankin jama’a na kasar da hukumar kula da hada-hadar kudade ta kasar suka fitar, ta bayyana cewa, taimakon kudi mai karfi zai tafi ga kamfanoni masu zaman kansu, musamman kanana, da matsakaita, da kuma wadanda ke da fasahohi kamar masana’antu masu fitar da karancin hayakin carbon mai gurbata muhalli.

Takardar sanarwar ta jaddada bukatar saukaka hanyoyin samun kudade daban-daban da suka haɗa da rance, da takardun lamuni da zaɓuɓɓukan hannun jari. Ta kuma bukaci kokarin habaka tallafin bashi ga masu neman lamuni a karon farko, da karfafa cibiyoyi na masu zuba jari da za su haɗa da hannayen jarin kamfanoni masu zaman kansu, da tallafawa kamfanoni masu zaman kansu dake cikin jerin kasuwannin hannun jari da yin haɗaka da sayarwa.

Za a yi amfani da manufofin kuɗi, da matakan tallafin da cibiyoyi na inshora, don tattara shirye-shiryen cibiyoyin hidimomin kuɗi da nufin biyan bukatun kamfanoni masu zaman kansu.

Wannan mataki, ya biyo bayan alkawarin da kasar Sin ta yi a farkon wannan shekarar, na bunkasa tattalin arzikin sassa masu zaman kansu, inda hukumomi suka sha alwashin kyautata yanayin kasuwanci, da kara ba da goyon baya ga manufofi, da karfafa matakan samar da lamuni kamar yadda doka ta tanada.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ma, mahukuntan kasar Sin, sun fitar da wani kundi mai kunshe da tsare-tsaren bunkasa tattalin arzikin sassa masu zaman kansu, ta hanyar kyautata yanayin gudanar da kasuwanci, da inganta manufofin daka iya tallafawa wannan kuduri, da karfafa tsarin shari’a wanda zai samar da tabbaci ga ci gaban fannin. 

Kundin ya bayyana yadda gwamnati za ta taimakawa ci gaba, da kyautata, tare da karfafa tattalin arzikin sassa masu zaman kansu, ta yadda sassan za su taka muhimmiyar rawa wajen ingiza farfadowar kasar ta Sin. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)