logo

HAUSA

Shugaban Najeriya zai gabatar da shawarar samar da karin tallafin kudi da fasaha a taron COP28

2023-11-29 11:03:03 CMG

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, na shirin gabatar da jawabi a taron bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 28 da ke tafe, a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda zai nemi bukatar karin tallafin kudi da fasaha ga kasashe masu tasowa da ke fama da tasirin sauyin yanayi.

Ajuri Ngelale, babban mai magana da yawun shugaban kasar shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, yana mai cewa shugaba Tinubu zai kuma bayyana matsayar Najeriya, kan batutuwa daban-daban da suka hada da makamashin da ake iya sabuntawa, da samar da kudaden tunkarar matsalar sauyin yanayi, a taron shugabannin kasashen duniya da zai gudana a ranar 1 zuwa 2 ga watan Disamba bisa taken "hada kai, yin aiki, da samun sakamako."

Ngelale ya bayyana cewa, bisa la’akari da mummunan tasirin sauyin yanayi da Najeriyar ke fuskanta, kamar kwararowar hamada,da ambaliyar ruwa,da zaizayar kasa,da fari, da matsalar tsaron kasa da ke tasowa daga wannan tasiri, shugaba Tinubu zai kara yawan damar da dandalin ya samar, na bayar da shawarar kara tallafin kudade da fasaha ga kasashe masu tasowa, inda zai tunatar da kasashen da suka ci gaba kan alkawarin da suka yi na bayar da dalar Amurka biliyan 100 a duk shekara, domin tallafawa shirye-shiryen da kasashe suka tsara, don magance kalubale masu alaka da matsalar sauyin yanayi. (Ibrahim)