logo

HAUSA

Ghana ta lashi takobin ci gaba da aiwatar da manufar kudi mai tsauri

2023-11-28 11:07:01 CMG Hausa

Babban bankin kasar Ghana, ya yi alkawarin ci gaba da aiwatar da manufar kudi mai tsauri cikin dogon lokaci duk da raguwar matakin hauhawar farashin kayayyaki cikin watanni 3 da suka gabata.

Gwamnan babban bankin Ernest Addison ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a jiya, bayan kammala taron da kwamitin kula da manufofin kudi na bankin ya yi domin nazartar tattalin arzikin kasar.

Bisa matsayin da bankin ya dauka, gwamnan ya sanar da matakin kwamitin na ci gaba da aiwatar da manufar kaso 30 na mafi karancin kudin ruwa. (Fa’iza Mustapha)