logo

HAUSA

Kungiyoyin fararen hula na Nijar sun bukaci da a janye takunkumin CEDEAO dana UEMOA da aka sanya wa Nijar

2023-11-28 09:09:03 CMG Hausa

A ranar jiya da yamma ne, wani kawancen kungiyoyin fararen hula na ceton kasa da dogaro da kai suka fitar da wata sanarwar, inda suka yi kira ga shugabannin yammacin Afrika na CEDEAO da UEMOA da su gaggauta janye takunkumin da suka kakabawa Nijar kafin taron shugabannin ECOWAS na ranar 10 ga watan Disamba mai zuwa.

Daga birnin Yamai, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Ita dai wannan sanarwa mai kama da kashedi zuwa ga shugabannin kungiyar CEDEAO ko ECOWAS, shi ne da su canja salonsu game da kasar Nijar, idan ba haka ba, a cewar kawancen kungiyoyin fararen hula, to ya zama dole ga Nijar da ta janye daga cikin wadannan kungiyoyin yammacin Afrika, tare da yin kira ga shugabannin Nijar, da su hada karfi da karfe da kasashen Mali da Burkina Faso domin kafa kundin kansu na bai daya, in ji mai magana da yawun kawancen kungiyoyin fararen hula na FPS.

“Muna kira ga ’yan Nijar su fito dafifi mu yi jerin gwano daga dandalin ‘Place Toumo’ mu zo nan mahadar hanyoyi ta ‘Rond-point Escadrille’, mu tambayi ECOWAS da sauran shugabannin Afrika wadanda suke karkashin Faransa su dage takunkumin da suka sanya ma Nijar nan take, idan ba su yi shi ba muna kira ga gwamnatinmu, da sojojin Nijar da ke cikin kwamitin ceton kasa na ‘Conseil National Sauvegarde de la Patrie’ cewa da CNSP daga ranar nan mu fara janye Nijar daga cikin ECOWAS daga cikin UEMOA kuma daga cikin ‘FRANCOPHONIE’ mu koma tare Mali da Burkina Faso mu kafa kudinmu na kanmu tun da ba mu ga abin da zama cikin CEDEAO ya janyo mana ba illa wahala.”

Kwanaki masu zuwa za su nuna mana ko yaya za ta kasancewa dangantaka tsakanin Nijar da kungiyoyin kasashen yammacin Afrika na CEDEAO da na UEMOA, za’a raba gari ko a’a.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.