logo

HAUSA

Guterres: Wajibi ne shugabannin duniya su kawo karshen mummunan yanayin dumamar yanayi a taron COP28

2023-11-28 10:52:51 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya jaddada cewa, akwai bukatar shugabannin kasashen duniya da za su halarci taron sauyin yanayi na COP28 na wannan mako, da su dakile ci gaban mummunan dumamar yanayi da ake fuskanta, kafin a fuskanci wani muhimmin yanayi.

Babban jami’in na MDD ya bayyana haka ne, yayin da yake yiwa manema labarai karin haske a hedkwatar MDD da ke New York, bayan da a karshen mako ya ganewa idonsa yadda curin dutsen kankara ke saurin narkewa a Antatika, saurin da ya ninka sau uku fiye da yadda ake gani a farkon shekarun 1990. 

An shirya gudanar da taron COP28, wanda ke nufin zama karo na 28 na babban taron kasashen duniya kan tsarin sauyin yanayi na MDD a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga watan Disamba.

Ya kara da cewa, mummunan yanayi na zafi na nufin yadda yanayin zafi ke karuwa fiye da kima, yayin da kankara ke raguwa ga kuma yanayi mai tsanani.

Yana mai cewa, kowa ya san mafita. Tilas ne shugabanni su dauki mataki don takaita karuwar yanayin zafin duniya zuwa ma’aunin digirin Celcius 1.5, da kare mutane daga matsalar yanayi, da kawo karshen amfani da makamashin dangin kwal, mai da iskar gas dake gurbata muhalli. (Ibrahim)