Innocent Odoh: Zan yi kokarin gabatar da rahotanni game da hadin-gwiwar Sin da Afirka
2023-11-28 15:29:46 CMG Hausa
Innocent Odoh, dan jarida ne dake aiki a gidan jaridar Leadership Newspapers dake tarayyar Najeriya. Kwanan nan ya kammala wani horo a fannin aikin jarida na tsawon watanni uku a kasar Sin.
Kafin ya koma gida Najeriya, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da shi a birnin Shanghai, a lokacin da shi da abokan karatunsa daga kasashe daban-daban suke ruwaito rahotanni dangane da bikin CIIE, wato bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na shida.
Mista Innocent ya bayyana ra’ayinsa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka, musamman karkashin BRI, wato shawarar “ziri daya da hanya daya”, da yadda ya kalli rayuwa, da yanayin aiki, gami da halayen mutanen kasar Sin.
A karshe, Innocent ya nuna kyakkyawan fatansa ga hadin-gwiwa, da mu’amalar kasar Sin da kasashen Afirka a nan gaba. (Murtala Zhang)