Sin da Japan da Koriya ta Kudu sun sake karfafa huldar diflomasiyya
2023-11-27 21:29:59 CMG Hausa
Bayan fiye da shekaru hudu, ministocin harkokin wajen kasashen Sin, Japan, da Koriya ta Kudu sun sake ganawa. A ran 26 ga wata, a gun taron ministocin harkokin wajen Sin da Japan da Koriya ta Kudu karo na 10 da aka yi a birnin Busan na kasar Koriya ta Kudu, kasashen uku sun cimma jerin matsaya kan zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu, tare da yin musayar ra'ayi kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya da suka shafi kasashen. Galibin ra'ayin jama'a na ganin cewa, taron ministocin harkokin wajen kasashen uku ya samar da yanayi da mataki na gaba ga taron shugabannin kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu.
Hakika, akwai alaka na dogaro da juna da moriyar juna tsakanin Sin, Japan, da Koriya ta Kudu. Jimillar yawan jama'a da GDP na kasashen uku sun kai kusan kashi 70 cikin dari da kashi 90 cikin dari na gabashin Asiya. Kasashen uku suna goyon bayan ra'ayin bangarori daban-daban da cinikayya cikin 'yanci, wadanda su ne kashin bayan tattalin arzikin yankin. (Yahaya)