logo

HAUSA

Ana gaggauta daukar matakan shawo kan mummunan tasirin ambaliya a Somaliya

2023-11-27 10:07:53 CMG Hausa

Gwamnatin Somaliya da hukumomin ba da agajin jin kai na kara azamar gudanar da ayyukan rage radadin mummunan tasirin ambaliyar ruwa, wadda ta haifar da asarar rayukan kusan mutane 100 a Somaliya. Cikin matakan da ake dauka dai har da na ceton rayuka a wuraren da ambaliyar ta yi kamari, bayan saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya, da ambaliya mai nasaba da sauyin yanayi na El Nino.

A ranar Asabar, hukumar yaki da bala’u ta kasar SODMA, ta ce a kalla mutane 96 sun rasu sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafi kimanin mutane miliyan 2.3.

Tuni dai MDD ta yi gargadin cewa, mummunar ambaliyar ruwan ta baya bayan nan, ta ta’azzara matsalar yunwa dake addabar mutane a Somaliya, inda ake hasashen kusan mutane miliyan 4.3 na iya fuskantar matsananciyar yunwa nan da karshen shekara. Kaza lika, ambaliyar ta lalata ababen more rayuwa, tare da dakatar da hada hadar cinikayya, da harkokin ilimi, da hidimomin samar da abinci.

Da yake tsokaci game da hakan, kwamishinan SODMA Mohamuud Moalim, ya ce sama da mutane 900,000 sun rasa matsugunnansu a sassa da dama na kasar, yayin da gwamnati da hukumomin ba da agajin jin kai ke ta matsa kaimin ceton wadanda suka makale a wurare daban daban sakamakon ibtila’in.

Hukumomin ba da agajin jin kai na cewa, ambaliyar ta kwanan nan na cikin munanan bala’u da suka aukawa Somaliya cikin shekarun baya bayan nan, inda al’ummun kasar da dama suka tsinki kan su cikin mummunan tasirin sauyin yanayi.  (Saminu Alhassan)