logo

HAUSA

Hamas ta saki kashi na uku na mutanen da take tsare da su

2023-11-27 09:58:52 CMG Hausa

A jiya ne, baraden Al-Qassam, reshen kungiyar Hamas masu dauke da makamai, ta sako kashi na uku na mutanen da ta yi garkuwa da su a zirin Gaza, karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta wucin gadi da suka cimma da Isra'ila.

A halin da ake ciki kuma, rundunar sojin Isra'ila a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta tabbatar da cewa, ta karbi mutane 13 da Hamas din ta sako a hannun kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa.

A wani labarin kuma, sashen kula da fursunoni na kungiyar ’yantar da Falasdinu, ya fitar da jerin sunayen fursunonin Falasdinawa 39 da aka sako a yammacin jiya

Majiyoyi na Palasdinawa na cewa, masu shiga tsakani na kokarin ganin an tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta da aka cimma a halin yanzu.

Majiyar wadda ta bukaci a sakaye sunanta, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasashen Qatar da Masar sun mika daftarin yarjejeniya ga Isra'ila da Hamas kan batun tsawaita wa'adin tsagaita wutar da zai kare a yau Litinin, da kuma samar da damar musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fada a cikin wata sanarwa ta kafar bidiyo jiya da dare cewa, mai yiwuwa ya amince da tsawaita tsagaita wuta na ’yan kwanaki, idan har Hamas za ta sako wasu karin mutanen da ta yi garkuwa da su.

A halin da ake ciki kuma, wata sanarwa daga wakilin Hamas ta bayyana cewa, Hamas na neman tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta na fiye da kwanaki hudu da tun farko aka cimma da Isra'ila. (Ibrahim Yaya)