logo

HAUSA

Ding Ping, yar kasuwa ce da ta dawo daga ketare, wadda ke son ba da gudummawarta wajen kare gine-ginen zamanin da na kasar Sin

2023-11-27 19:20:39 CMG Hausa

Yar kasar Sin Ding Ping ta kama kan hanyar gudanar da kasuwanci tun bayan kammala karatunta a jami'ar Leeds da ke Burtaniya a shekarar 2021. A cikin shekaru biyu da dawowar ta daga kasar waje bayan kammala karatunta, wadda tun farko ta yi digiri a fannin tattalin arziki, kwatsam ta shiga sana’ar gyaran gine-gine na zamanin da, har ma ta kafa kamfanin ta. 

Ding Ping ta ce a zahiri ta soma sha'awar kayan tarihi da gine-ginen zamanin da ne tun lokacin da take karatu a Burtaniya.

“Lokacin da na je gidan ibada na Confucius a karon farko tun ina karama, na ji kaunar su sosai, kuma nan da nan wadannan tsoffin gine-ginen suka jawo hankali na. Daga baya, a lokacin da nake karatu a Burtaniya, na kuma ji dadin yawo a kasuwannin tsaffin kayayyaki, don kallon kayayyaki daban-daban kamar su tsoffin tsabar kudi, agogon aljihu, kayan tarihi, da lu'ulu'u, da dai sauransu. A ko da yaushe ina jin cewa akwai labarai marasa iyaka a bayan wadannan tsoffin abubuwa, don haka wadannan abubuwan na iya ba ni sha'awa kan sana’ar da nake gudanarwa a yanzu.”

Amma, ba abu ne mai sauki ba canzawa daga sha'awar tsoffin abubuwa zuwa shiga sana’ar gyaran gine-gine na zamanin da.

“Kamfaninmu kamfani ne na kasuwanci, kuma a farkon bude shi, ba mu fahimci fannonin fasaha da yawa ba. Na hadu da wani dattijo babba a lokacin, wanda kuma shi ne jagora na wajen shiga wannan masana’anta, bisa taimakonsa na yi sauri na shiga wannan sana’ar. A hakika, aikin gyaran gine-gine na zamanin da, ya fi wuya bisa sake yin gine-gine masu salon gargajiya, a cikin wannan tsari, masu fasaha suna bukatar yin iyakacin kokari don adana bayanan tarihi, da kimarsu ba tare da canza yanayinsu na asali ba. Kasar Sin tsohuwar kasa ce ta wayewar kai mai tarihin shekaru 5,000, tana da dogon tarihi da kyawawan al'adu. Don haka, a matsayina na matashiya, ina jin nauyin dake bisa wuya na na rayawa, da kuma gadon al'adu. "

Ding Ping ta ce, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kamfanin da ta kafa ya shawo kan matsaloli daban-daban, kuma a hankali ya hau kan hanyar da ta dace, yana kuma da ma'aikata sama da 50, ciki har da ma'aikatan fasaha. A yayin da take bincike a sana’ar, ta samu ta ta fahimtar.

A halin yanzu, kamfanin ya jawo hankalin mutane da yawa da suka dawo daga kasashen waje bayan kammala karatunsu, wadanda kuma ke da kuzari da hangen nesa.

"Ko da yake sana'ar gyara gine-gine da kayan al'adu na zamanin da, na bukatar bin al'ada ta fuskar fasaha, amma daliban da suka taba karatu a kasashen waje na iya samun sabbin ra'ayoyi masu bambanci. Gyaran gine-gine na zamanin da a hakika wani fanni ne da ba a san shi sosai ba, Ina ganin idan ana son habaka wannan masana'antar cikin dogon lokaci, ana bukatar tunani iri-iri na daliban da suka dawo daka kasashen waje, kuma ina fatan karin daliban za su iya mai da hankali kan wannan sana’ar. "

A yayin da take zantawa da takwarorinta, Ding Ping ta jajirce, tare shan alwashin fadada aikin gyaran gine-ginen zamanin da a kasashen ketare.

"Ina ganin akwai tsoffin gine-gine da yawa a kudu maso gabashin Asiya. Shin za a iya fitar da fasahar mu ta gyaran tsoffin gine-gine zuwa ketare? A gaskiya ma, ina aiki a wannan fanni a yanzu, ina fatan nan gaba, za mu iya samun karin damammaki na gyara gine-ginen zamanin da, ko a kudu maso gabashin Asiya ko kuma a Turai, ta haka za mu iya yada kyawawan gine-gine da fasahar kasar Sin a kasashen waje. "

Ding Ping ta ce a lokacin da ta shiga sana’ar gyaran gine-gine na zamanin da, bata takaita da kasancewa ‘yar kasuwa ba, har ma ta zama mai kiyayewa, da kuma yada al'adun kasar Sin. Yayin da take tunawa da yanayin da ta kai wasu abokan kasashen waje ziyartar gine-ginen zamanin da na kasar Sin a shekarar bana, ta ce tana fatan karin abokai na kasashen waje za su iya ganin kyawawan halayen kasar Sin, da hikimar Sinawa da ke bayan wadannan tsoffin gine-gine.

“Baya ga ba da labaran tarihi, zan kuma gaya musu wasu abubuwa, kamar me ake kiran irin wannan tsarin gine-gine? Mene ne takamaiman amfaninsa? Alal misali, lokacin da ya ga wani irin tsarin gine-gine na musamman na kasar Sin, wani aboki daga kasar Jamus ya tambaye ni, 'Shin da gaske ne babu kusa ko daya a ciki?' Gaskiya suna cika da sha’awa sosai, su kan yi shakkun yaya ake yi? A yayin wannan aikin, na ba su damar fahimtar hikima, da fasahar masu sana'ar a zamanin da a kasar Sin, kuma na yi alfahari da kaina."

Ding Ping tana da cikakken tsarin bunkasa aikinta a nan gaba. Maimakon fadadawa cikin sauri, ta fi son ganin cewa ita da kungiyarta su samu ci gaba a hankali a hankali. Ta kuma yi fatan samun karin matasa da za su shiga cikin kungiyarta, tare da yin amfani da kuruciyarsu wajen ba da gudummawar da ta dace, a fannin kare gine-ginen zamanin da da kuma gadon al’adu.

“Gyarawa da kare gine-ginen zamanin da na kasar Sin, a hakika shi ne gado da kare kayan tarihi. Ko da yake gyare-gyaren na iya hadawa da rufin sama ko bango, amma aikin ya ma kunshi abubuwa daban-daban da suka shafi tarihi, da gine-gine, da fasaha da dai sauransu. A nan gaba, baya ga kara habaka wasu kasuwanni, kuma yana da muhimmanci a horar da gungun matasa masu fasaha. Muddin suna da sha'awa, ba su damar shiga wannan sana’a na iya farfado da kayayyakin al'adu. "