logo

HAUSA

Manufar Sin Ta Baiwa Kasashe Damar Shigowa Kasarta Ba Tare Da Biza Ba Za Ta Bunkasa Mu'amala Tsakanin Jama'a Da Jama'a

2023-11-27 16:55:39 CMG HAUSA

DAGA Muhammed Yahaya

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a ranar 24 ga watan Nuwamba cewa, kasar Sin ta yanke shawarar gwada tsarin baiwa karin kasashe damar shiga kasar ba tare da biza ba, wanda ya shafi tsawaita zaman matafiya masu rike da fasfo na kasa da kasa daga kasashe shida, wato Faransa, Jamus, Italiya, Netherlands, Spain, da Malaysia.

 

Wato abin nufi shi ne, daga ranar 1 ga watan Disamba, 2023, zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024, ’yan wadannan kasashe guda shida da ke shiga kasar Sin don kasuwanci, da yawon bude ido, da ziyartar ’yan uwa da abokan arziki, ko kuma yada zango na tsawon kwanaki 15, ba za su bukaci biza ba. Duk da cewa shirin na gwaji ne kamar yadda aka tsara. Amma idan shirin ya yi nasara kuma bai haifar da cikas ko wasu batutuwan da za su shafi zamantakewar al'umma ba, to ba mamaki shirin zai ci gaba da zama na dindindin.

Shirin yana da mahimmanci ta hanyoyi da yawa, yawancin tsarin shiga kasa ba tare da biza ba, ana gudanar da shi ne bisa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, wanda ke nufin kasar mai shigowa ita ma dole ta tanadi kwatankwacin tsarin ga Sinawa.

Hikimar dake cikin yadda kafofin watsa labaru suka fassara wannan matakin na Beijing shi ne, tsarin na da manufar jawo hankalin masu yawon bude ido daga wadannan kasashe. Saboda shekaru uku da aka yi ana fama da cutar ta COVID-19 ya yi tasiri sosai ga masana'antar yawon shakatawa ta duniya, saboda haka wannan manufa ce da za ta dora wannan fannin tattalin arziki bisa kyakkyawar turba.   

A farkon watan Nuwamba, kasar Sin ta fadada manufofinta na yada zango a kasar ba tare da biza ba zuwa ga kasashe 54. Manyan jami’an gwamnatocin kasashen waje da suka hada da ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna, da jakadiyar Jamus a kasar Sin Patricia Flor, sun yaba da wannan yunkurin inda suka yi tsokaci cewa, "Wannan yunkuri ne mai kyau kuma zai saukaka balaguro zuwa kasar Sin ga ’yan kasashen waje da dama da ba a taba ganin irinsa ba.

A ganina, wannan sabon matakin ya wuce kawai don jawo hankalin masu yawon bude ido. Mataki ne dake nuni da yadda kasar Sin ta ci gaba da bude kofa ga kasashen duniya, da ci gaba da cudanya da sauran kasashen duniya, da ci gaba da yin mu'amala tsakanin jama'a da duniya. Fatana a nan shi ne a nan gaba, kasar Sin za ta shigar da karin kasashe masu tasowa cikin wannan tsarin musamman ma kasashen nahiyar Afirka. (Muhammed Yahaya)