logo

HAUSA

Gwamnatin Sudan da IGAD sun amince da kiran taron gaggawa game da rikicin Sudan

2023-11-27 14:25:01 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Sudan, ta ce shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Abdelfattah Al-Burhan, da babban sakataren kungiyar shugabannin kasashen gabashin Afirka ko IGAD Workneh Gebeyehu, sun amince su kira taron gaggawa karkashin kungiyar IGAD, domin tattauna batutuwan da suka shafi kara rincabewar rikicin Sudan.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin Sudan ta fitar, ta ce shugaba Al-Burhan da mista Workneh, sun zanta da juna, yayin wata tattaunawa da shugaban kasar Djibouti Ismail Omar. A lokacin ganawar tasu, Al-Burhan da Workneh sun maida hankali ga tattaunawar da ake yi a Saudiyya, inda wakilan dakarun sojin kasar da na tawagar ko ta kwana ta RSF ke ganawa kai tsaye.

Tattaunawar bangarorin biyu na zuwa ne a gabar da rikicin Sudan ke kara kazanta, kuma dakarun RSF ke fadada tasirinsu a sassan birnin Khartoum da yankin Darfur, inda suka kwace iko da jihohi 4 cikin 5, kamar dai yadda jaridar Sudans Post ta wallafa.

A wani ci gaban kuma, majalissar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar AU ta fitar da wata sanarwa, wadda ke Allah wadai da rikicin dake ci gaba da gudana a Sudan, tana mai kira da a gaggauta tsagaita bude wuta ba tare da gindaya wani sharadi ba.  (Saminu Alhassan)