logo

HAUSA

Shugaban majalisar mulki ta rikon kwarya ta Sudan zai tattauna yanayin kasarsa da shugaban Djibouti

2023-11-26 15:59:13 CMG Hausa

A yau Lahadi 26 ga wannan wata ne shugaban majalisar mulki ta rikon kwarya ta kasar Sudan kuma babban kwamandan dakarun kasar Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan ya tashi zuwa kasar Djibouti domin gudanar da ziyarar aiki, inda zai yi shawarwari da shugaban kasar Ismail Omar Guelleh, musamman ma kan yanayin da Sudan ke ciki.

A halin yanzu, shugaban Djibouti Guelleh shi ne shugaban kungiyar IGAD wato kungiyar raya yankin gabashin Afirka, kwanan baya ya gabatar da shawarar kirar taron kolin gaggawa na kungiyar IGAD a farkon watan Disamban dake tafe, domin daidaita rikici tsakanin dakarun Sudan, da kuma sassauta yanayin jin kai a kasar.

Rikici ya barke tsakanin dakarun gwamnatin kasar Sudan da rundunar RSF ta kasar a birnin Khartoum, fadar mulkin kasar a ranar 15 ga watan Afirilun bana, daga baya ya bazu zuwa sauran sassan kasar, har yanzu ba a kawo karshensa ba tukuna. Ya zuwa ranar 29 ga watan Oktoban da ya gabata, ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar da wata sanarwa, inda ta sanar da cewa, dakarun gwamnatin kasar Sudan da rundunar RSF ta kasar sun sake yin shawarwari a birnin Jeddah domin tsagaita bude wuta karkashin shiga tsakanin wasu kasashe da IGAD. (Jamila)