logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da takwarorinsa na Japan da Koriya ta Kudu

2023-11-26 15:52:30 CMG Hausa

A jiya Asabar 25 ga wannan wata ne mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Japan da kuma Koriya ta Kudu a birnin Busan na kasar Koriya ta Kudu.

Yayin da yake halartar taron, Wang Yi ya yi ganawa da ministar harkokin wajen kasar Japan Yoko Kamikawa, inda manyan jami’an biyu suka amince da shirya sabon zagaye na tattaunawa tsakanin manyan jami’an tattalin arziki da al’adu, tare kuma da shirya shawarwari bisa manyan tsare-tsare kan batutuwan game da tsaro da harkokin waje tsakanin kasashen biyu.

Kana Wang Yi ya yi ganawa da takwaransa na Koriya ta Kudu Park Jin, inda suka tabbatar da huldar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin Sin da Koriya ta Kudun, haka kuma suka nuna anniyarsu ta ciyar da huldar gaba yadda ya kamata.

Yayin gasawar ta su, Wang Yi ya yi tsokaci cewa, ya dace kasashen biyu wato Sin da Koriya ta Kudu su yi kokari tare domin yin adawa da yunkurin siyasantar da batun tattalin arziki da kimiyya da fasaha, ko kuma tattauna kan tsaron kasa bisa fakewa da batun tattalin arziki da cinikayya ta yadda za a sa kaimi ga ci gaban hadin gwiwar tattalin arziki da ciniyya tsakanin sassan biyu. (Jamila)