Tanzaniya ta yaba wa kasar Sin game da hadin gwiwa a fannin ilimin fasaha da na sana’a
2023-11-26 16:07:49 CMG Hausa
A jiya Asabar ne cibiyoyin Sin da Tanzaniya masu kula da harkokin koyar da fasahohi da koyar da sana’o’i na kasashen biyu (TVET) suka yi taro don karfafa hadin gwiwa wajen samar da ilimi da kyawawan ayyuka.
Jami'ai daga cibiyoyin TVET na kasashen biyu sun hallara a birnin Dar es Salaam cibiyar kasuwancin kasar Tanzaniya yayin taron na karawa juna sani na TVETn Sin da Tanzaniya kan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu kan bunkasa matsayin sana'o'i.
Franklin Rwezimula, mataimakin sakatare a Ma'aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta kasar Tanzania, ya ce Sin da Tanzania na iya samar da sabbin kwararrun ma’aikata da zasu sa kaimi ga ci gaban kirkire-kirkire, harkokin kasuwanci, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa ta hanyar hadin gwiwar da TVET ta samar.
Rwezimula ya ce, hadin gwiwar da kasar Sin ba kawai za ta inganta TVET ba, har ma za ta samar da kwararrun ma’aikata, da jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje, ciki har da jarin Sinawa a Tanzaniya. (Yahaya)