logo

HAUSA

Isra’ila ta karbi mutanen da kungiyar Hamas ta saki

2023-11-25 16:53:50 CMG Hausa

Kafofin watsa labaru na kasar Isra’ila sun ruwaito wani jami’in hukumar tsaron kasar na cewa, a jiya Juma’a, kungiyar Hamas ta saki mata da yara 13 da ta yi garkuwa da su, kuma hukumar tsaron kasar Isra’ila ta karbe su.

Shi ma wani jami’in Palesdinu ya bayyana a jiyan cewa, Isra’ila ta saki Palesdinawa 39 da take tsare da su, wadanda suka hada da mata 24 da kananan raya 15, yawancinsu kuma sun fito ne daga yankin yammacin gabar kogin Jordan da gabashin Kudus.

Hukumar kula da harkokin jin kai ta MDD ta sanar a jiya cewa, bayan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta Palesdinu, an tura motoci 200 dauke da kayayyakin taimako zuwa yankin iyakar Rafah, kana an shigar da makamashi lita dubu 129 da manyan motoci 4 masu dauke da iskar gas zuwa zirin Gaza.  Haka kuma an kwashe mutane 21 da suke cikin yanayin rashin lafiya mai tsanani daga arewacin zirin Gaza. Bugu da kari, mutane fiye da dubu 100 sun samu abinci da ruwan sha da magani da sauran kayayyakin taimako. (Zainab)