logo

HAUSA

Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina ya sake lashe zaben shugaban kasa

2023-11-25 20:56:52 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina ya sake lashe zaben shugaban kasar bayan samun kaso 50 na kuri’un da aka kada.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ce ta sanar da haka cikin sakamako na farko da ta fitar a yau.

Madagascar ta gudanar da zagaye na farko na zaben shugaban kasa a ranar 16 ga wata domin zaben shugabanta a wa’adin shekaru 5 masu zuwa tsakanin ‘yan takara 13. (Fa’iza Mustapha)