logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Bukaci Japan Ta Amince Kasashen Duniya Su Sa Ido Kan Yadda Take Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku

2023-11-25 16:25:03 CMG Hausa

Kasar Sin ta sake jaddada matsayarta kan matakin Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliyar tashar Fukushima a cikin teku, tana mai bukatar Japan din ta amince kasashen duniya su sa ido kan shirin nata.

Wakilin dindindin na kasar Sin a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) Li Song ne ya bayyana haka a jiya, yayin taron kwamitin gwamnoni na hukumar.

A cewarsa, Japan ta yi watsi da korafin kasa da kasa da ma adawa mai karfi da kasashen suka nuna, inda ta kaddamar da shirinta na zuba ruwan dagwalon nukiliyar tashar Fukushima cikin teku.

Ya ce, shirin na Japan ba batu ne na cikin gida ba, batu ne da ya shafi amincin nukiliya da muhallin teku na duniya da lafiyar al’umma da muradun kasa da kasa, yana mai cewa, Sin na adawa da shirin kuma tana kira ga Japan ta dakatar da shi.

Bugu da kari, ya bukaci hukumar IAEA ta tuntubi kasashe mambobinta kana ta karfafa shirin da zai ba kasashen damar sa ido yadda ya kamata kan shirin na Japan, bisa daukaka adalci da tsare gaskiya da bin matakan kimiyya. (Fa’iza Mustapha)