logo

HAUSA

Cike Gibin Ababen More Rayuwa A Afrika Na Da Muhimmanci Wajen Cimma Burikan Tunkarar Sauyin Yanayi

2023-11-25 15:57:30 CMG Hausa

Kwamishinar Tarayyar Afrika (AU) mai kula da ababen more rayuwa da makamashi, Amani Abou-Zeid, ta ce cike gibin ababen more rayuwa da kara zuba jari a bangaren makamashi mai tsafta, na da matukar muhimmanci wajen taimakawa kasashen Afrika cimma burikan shawo kan matsalar sauyin yanayi.

Amani Abou-Zeid ta bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai a daren ranar Alhamis, tana mai cewa, nahiyar na fuskantar gagarumin gibin ababen more rayuwa, lamarin dake kawo tsaiko ga bunkasar tattalin arziki da ci gabanta.

Ta kara da cewa, samun ababen more rayuwa da nahiyar ke bukata na bukatar kara zuba jari a bangarori kamar na sufuri da makamashi da fasahohin zamani, tana mai cewa, wadannan bangarori su ma na da matukar muhimmanci ga komawar nahiyar zuwa ga amfani da makamshi mai tsafta da samun ci gaba mai dorewa.

A cewarta, yayin taron MDD kan sauyin yanayi karo na 28 wato COP28, shugabannin Afrika za su bayyana muhimmancin kara zuba jari da bukatar samun fasahohi domin gaggauta komawar nahiyar kan makamashin mai tsafta.

Jami’ar ta ce, yayin taron COP28 da zai gudana makon gobe a Hadaddiyar Daular Larabawa, kasashen Afrika za su nemi hadin gwiwa da jari daga sauran kasashen duniya domin kara samun shirye-shiryen da za su cike gibin ababen more rayuwa a nahiyar, da fadada damar samun makamashi mai tsafta da bunkasa hade nahiyar ta hanyar fasahohi. (Fa’iza Mustapha)