Shugaban Africa CDC Ya Yaba Da Hadin Gwiwar Sin Da Afrika A Bangaren Kiwon Lafiyar Al’umma
2023-11-24 21:18:00 CMG Hausa
Darakta janar na cibiyar kandagarki da takaita yaduwar cututtuka ta Afrika (Africa CDC) Jean Kaseya, ya yaba da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika a bangaren kiwon lafiyar al’umma.
Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan, Jean Kaseya ya bayyana taimakon horar da jami’ai da Sin take yi a matsayin sakamakon kyakkyawan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika a bangaren lafiya.
Jean Kaseya ya kara da cewa, nahiyar Afrika da ta dade tana fama da barkewar cututtuka, na matukar bukatar inganta tsarinta na dakile yaduwar cututtukan.
Ya ce, hadin gwiwar da Sin ta ba cibiyar Afrika CDC damar taka rawa wajen tsara aikin kandagarkin cututtuka da sa ido da takaita yaduwarsu a nahiyar, inda a kan samu barkewar sabbin cututtuka biyu a kowanne mako.
Ya ci gaba da cewa, dakin gwaji na zamani da Sin ta taimaka wajen samarwa, wanda aka kaddamar a baya-bayan nan a harabar hedkwatar cibiyar Afrika CDC a Addis Ababa, shi ne sakamako na baya-bayan nan na hadin gwiwar Sin da Afrika a bangaren kiwon lafiyar al’umma. (Fa’iza Mustapha)